Za'a fitar da sabon farashin litar Man Fetur a Najeriya.

 Za'a fitar da sabon farashin litar Man Fetur a Najeriya. 



A yanzu haka manyan 'yan kasuwar mai na Najeriya, sunyi zaman dirshan suna jiran Dangote ya fitar da farashin mai dinshi domin chanja akalar farashin litar Man Fetur a fadin Najeriya. 


'Yan kasuwar suna tsammanin Dangote zai basu farashin ta Dala ko kuma ta Naira. Masu hasashe sun tabbatar da cewa idan Dangote ya fitar da sabon farashin shi da kuma karbar kudaden biya ga dilolin da Naira, akwai yiwuwar a samu saukin farashi akan yadda farashin yake a yanzu. 


Yanzu dai zamu zubawa sarautar Allah ido muga me zai faru. Muna fatan Allah yasa farashin ya sauka, domin mu talakawa mu kara samun saukin rayuwa. 


Daga Comr Abba Sani Pantami

Post a Comment

0 Comments