ZIYARAR DAKTA AHMAD GUMI A IRAN.....
"Babban abin tsoron mafi yawan musulmi musamman Ahlus-Sunnah, shi ne aqidar Shi’a wadda ake ganin ta mayar da hankali wurin rarraba kan jama’a. Na tarar da jawabin shugaban ƙasa da kuma na Babban Sakatare Janar na Majalisar Dokoki DR. Hamid Shahriari yana karfafa gwiwa (akan haɗin kan Musulmi), a lokacin da suka bude jawabansu ciki har da Sahabbai a cikin girmamawa da addu'o'insu na alheri da sulhu.
Musulmai suna mu'amala sosai da ƙasashen yammacin duniya (Turawa) duk da halin da suke da shi na goyon bayan ɓatancin da ake yi wa Manzo Allah da sunan ƴancin fadin albarkacin baki. Irin wannan magana (na ɓatancin da suke wa Manzon Allah da Addinin Musulunci kuma muke mu'amalada su) Me zai hana (Muyi mu'amala da) Iran? (Wadda kawai saɓawa mukai akan fahimta).
Ina jinjina wa Iran bisa tsayin dakan da suka yi kan al'amuran ƙasa da ƙasa, da tsayin daka wajen fuskantar matsalar toshewar tattalin arziki (Na takunkumi da aka sanya musu), da zagon kasa (wajan kai musu hare-haren ta'addanci), da kokarin da suke yi na ganin sun kawo ci gaba a cikin mazhabobin Musulunci (wato haɗin kai a tsakanin Musulmi). (Kuma wannan gagarumin aikin da suke na haɗa kan Musulmi) Wannan umarni ne na Ubangiji na Musulunci".
Ahmad Gumi
Talata, 16 ga Janairu, 2024.
Kaduna
Fassara; Muhd Bala Afuwa
0 Comments