Africa ta sa baki kan hare-haren Isra'ila
Afirka ta Kudu ta jaddada cewa hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Rafah zai iya jawo kashe ƙarin ɗumbin mutane da lalata wurare.
Afrika ta Kudu ta buƙaci babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara matsin lamba ga Isra’ila domin ta dakatar da hare-haren da take kaiwa a birnin Rafah da ke kudancin Gaza.
Tuni Pretoria ta gabatar da kokenta dangane da Isra’ila a Babbar Kotun Duniya (ICJ) da ke Hague, inda take zargin hare-haren da Isra’ila ke kaiwa a Gaza laifukan yaƙi ne.
Har yanzu kotun ba ta yanke hukunci kan lamarin ba, amma a ranar 26 ga watan Janairu, ta bayar da umarni ga Isra’ila da ta tabbatar da kare fararen hula daga cutuwa da kuma barin kayan agaji shiga.
Sai dai duk da haka Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare haka kuma dakarun ƙasar na kai hare-hare a Rafah, inda rabin jama’ar Gaza mai mutum miliyan 2.4 suke neman mafaka sakamakon hare-haren na Isra’ila
0 Comments