Allah yayima Tsohon Gwamnan Yobe Bukar Abba Ibrahim rasuwa.
Tsohon Gwamnan Jihar Yobe da ke arewacin Nijeriya Sanata Bukar Abba Ibrahim ya rasu yana da shekara 75.
Rahotanni sun ce ya rasu ne ranar Lahadin nan a ƙasar Saudiyya bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Gwamnatin jihar Yobe ta tabbatar da rasuwarsa ta bakin Mamman Mohammed, mai magana da yawun Gwamna Mai Mala Buni.
"Sanata Bukar ya rasu yau a yayin da yake jinya a Saudiyya kuma za a binne shi a can," in ji sanarwar da Mamman Mohammed ya fitar.
Ya bar mata biyu da Æ´aÆ´a 17.
Ɗaya daga cikin matansa ita ceKhadija Bukar Abba Ibrahim, ƴar majalisar wakilan Nijeriya kuma tsohuwar ƙaramar minista a Ma'aikatar Harkokin ƙasar.
Kafin rasuwarsa ya kasance Gwamnan Jihar Yobe daga 1992 zuwa 1993, sannan ya sake jagorantar jihar a matsayin gwamna tun daga 1999 har zuwa 2007.
Marigayin ya wakilci Jihar Yobe a Majalisar Dattawan Nijeriya daga 2007 har zuwa 2019.
Taƙaitaccen tarihin marigayin
Bukar Abba ya soma karatunsa na firamare a 1957. A 1965, sai ya tafi Kwalejin gwamnati ta Maiduguri domin ci gaba da karatun sakandare. Marigayin ya shiga Jami’ar Ahmadu Bello a 1972 inda ya samu digiri kan Quantity Surveying.
Bayan nan sai ya ci gaba da digirinsa na biyu a Birtaniya tsakanin 1981 zuwa 1982.
Daga 1985 zuwa 1988 ya yi aiki a matsayin ma’aikacin gwamnatin jihar Borno inda har ya kai matakin kwamishinan ayyuka.
A Disambar 1991 watanni bayan Yobe ta samu jiha sai ya yi takarar gwamna inda ya ci zabe karkashin jam’iyyar SDP.
Ya rike wannan mukamin har zuwa lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin.
0 Comments