An guudanar da zanga-zangar 'tsadar rayuwa' a jihohin Nijeriya

An guudanar da zanga-zangar 'tsadar rayuwa' a jihohin Nijeriya

Ƙungiyar Ƙwadago a Nijeriya ta gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi dangane da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.

Ƙungiyar Ƙwadago a Nijeriya ta gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar domin nuna rashin jin daɗi dangane da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.

Ana gudanar da zanga-zangar ce duk da yunƙurin da gwamnatin tarayyar ƙasar ta yi na dakatar da ita.

Haka kuma zanga-zangar ta biyo bayan wa’adin mako biyu da ƙungiyar ƙwadagon ta bai wa gwamnatin tarayyar ƙasar domin ta samar da matakai waɗanda za su rage tsadar rayuwa a ƙasar.

Rahotanni daga ƙasar sun ce tun daga misalin 7:00 na safe masu zanga-zangar suka soma taruwa inda suke riƙe da alluna waɗanda ke da rubutu game da wahalwalun da ake fama da su a ƙasar.

A Jihar Legas, masu zanga-zangar sun taru a Ikeja ƙarƙashin gada kuma rahotanni sun ce ɗimbin jama’a ne suka taru.

A Jihar Oyo kuwa, mambobin na NLC sun taru a sakateriyar ƙungiyar da ke Agodi a Ibadan babban birnin jihar.

A Kaduna ma haka abin yake inda mambobin ƙungiyar suka taru a sakateriyar ƙungiyar.

Post a Comment

0 Comments