An kama 'ɗan bindigar da ya yi ƙaura daga Kaduna zuwa Kano don kafa sansani'


An kama 'ɗan bindigar da ya yi ƙaura daga Kaduna zuwa Kano don kafa sansani'

Rundunar ƴan sandan Nijeriya a Jihar Kano ta ce ta kama wani ƙasurgumin ɗan bindiga wanda ya shaida mata cewa ya yi ƙaura ne daga jihar Kaduna zuwa Kano don ya kafa sansanin ƴan bindiga a dajin Gwarzo zuwa Ƙaraye.

Sanarwar da rundunar ta fitar a ranar Litinin da maraice mai ɗauke da sa hannun mataimakin jami’in hulɗa da jama’a ASP Abdullahi Hussaini ta ce wata tawagar ƴan sanda da ke aikin leƙen asiri ce ta kama mutumin.

“A ranar 4 ga wata ne da misalin ƙarfe 5.40 na yamma, wata tawagar ƴan sanda da ke aikin leƙen asiri a ƙaramar hukumar Ƙaraye ƙarƙashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal, ta yi nasarar kama Isah Lawal mai shekara 33 ɗan asalin ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa an kuma samu shanu 55 da tumaki shida a wurinsa a samamen da ƴan sandan suka yi a kan iyakar jihohin biyu.

“A yayin bincike ne wanda ake zargin ya bayyana cewa sun gudu ne daga Sansanin Ƴan Bindiga na Maidaro a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a Jihar Kaduna saboda an kashe shugabansu Bashir, ɗan garin Malumfashi na Jihar Katsina a wani faɗa tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga biyu da aka yi.

Post a Comment

0 Comments