Ƴan sanda sunyi nasarar kama mutum 307 a yayin wani samame a Abuja

Ƴan sanda sunyi nasarar kama  mutum 307 a yayin wani samame a Abuja



Daga TRT Africa.

Kwamishinan ƴan sandan Abuja da kansa ya jagoranci kai samamen a Gidan Dambe da ke unguwar Dei-Dei inda aka kama mutum 307.

Rundunar ƴan sandan Nijeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar ta tabbatar da kama mutum 307 a wani samame da ta kai a Gidan Dambe da ke unguwar Dei-Dei inda ta ce jami’anta na rundunar operaton Velvet ne suka kai samamen.

Mai magana da yawun rundunar reshen Abuja SP Josephine Adeh ta tabbatar wa TRT Afrika cewa kwamishinan ƴan sandan Abuja ne da kansa ya jagoranci jami’an tsaro domin kai wannan samame, inda ta ce ana zargin masu aikata manyan laifuka kamar su garkuwa da mutane da fashi da makami da zuwa shaƙatawa a Gidan Damben.

“A lokacin samamen, an gano bindiga ƙirar pistol ɗaya da harsasai 15 daga wani Ibrahim Tukur wanda ya yi iƙirarin cewa shi ma’aikacin DSS ne,” in ji sanarwar da yan sandan suka fitar.

Rundunar ta ce sauran abubuwan da aka gano sun haɗa da babura da ƙulli-ƙulli na wiwi da wasu haramtattun kayayyaki.

Haka kuma akwai wasu kayayyaki masu daraja waɗanda ake zargin sato su aka yi daga jama’a da aka samu a hannun waɗanda ake zargin.

SP Adeh ta tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gudanar da bincike mai zurfi kan mutum 307 da aka kama inda ta ce waɗanda aka samu da laifi za a kai su kotu domin fuskantar hukunci.

Abuja babban birnin Nijeriya dai na neman zama matattarar masu aikata laifuka waɗanda suka haɗa da fashi da makami da garkuwa da mutane.

Ko a makon da ya gabata sai da rundunar ta ce jami'anta sun yi nasarar kashe gawurtattun masu garkuwa da mutane da dama da suka addabi wasu yankunan Abuja babban birnin ƙasar.

Haka kuma a watan Janairu rundunar ta tabbatar ceto akalla mutum 154 daga hannun masu garkuwa da mutane.

Post a Comment

0 Comments