Ansake rokon majalisar wakilan jihar Kano data yi duba akan kudurin soke masarautun Kano hudu domin dawo da khalifa sanusi a matsayin sarki.

Ansake rokon majalisar wakilan jihar Kano data yi duba akan kudurin soke masarautun Kano hudu domin dawo da khalifa sanusi a matsayin sarki.

Shugaban kungiyar Najeeb Abdulqadir Salati

Kungiyar nan da ta rubutawa majalisar dokokin jahar Kano wasika kan ta duba yiwuwar rushe masarautun Kano guda hudu, tare da rokon dawo da Sarkin Kano na14 Malam Muhammadu Sunusi ll, ta sake rokon majalisar data yi duba na tsanaki kan wancan roko nasu.

Kungiyar ta yi wannan kiranne ta bakin Shugaban kungiyar Najeeb Abdulqadir Salati, a wani taron manema labarai da ta gudanar a yau Asabar, inda ta nemi majalisar da ta sake nazari kan dalilan da suka Sanya aka cire tsohon Sarkin daga kan karagarsa, dakuma yin gaggawar daukar mataki.

Salati ya Cigaba da cewa dawo da Sarkin Kano Muhammad sunusi kan sarautar jahar Kano bawai zai gyara kuskuren da akayi a baya bane kadai, zai tabbatar da kokarin gwamnatin ne na tabbatar da doka da oda tare da adalci.

Post a Comment

0 Comments