Ansamu mace ta farko wacce ta Gama jami'a a jihar Katsina da sakamakon first class

Ansamu mace ta farko wacce ta Gama jami'a a jihar Katsina da sakamakon first class



A karon farko mace yar asalin jihar Katsina daga Funtua Maryam Hussaini ta kammala Jami'ar Yar'adua da sakamakon First Class a Public Administration

Maryam Hussaini dake Dutsen-Reme Funtua yankin karamar hukumar Bakori nan jihar Katsina, ta doke maza, inda Allah Ya bata ikon kammala Jami'ar ta Umaru Musa Yar'adua Katsina da sakamakon First Class a sashen koyon kimiyyar mulkin al'umma wato BSc Public Administration

Sakamakon First Class ba karamin abu bane da ba a samunsa da wasa, kuma ya fi karfin raggoon dalibi, duk wanda ke karatu a jami'o'i ko kwalejoji sun san da hakan, domin ƙa'idarsa sai dalibin dake cin A a kowane darasi tun daga farkon shigarsa har ya kammala shekara hudunsa, ko biyar a Jami'a, sannan ne zai sami irin wannan sakamakon na First Class wato ya kure, komai aka koya masa ya iya yana cin aƙalla maki 70 bisa dari

Post a Comment

0 Comments