Ƴansanda sun kama ƙarin mutum 24 kan zanga-zangar da aka gudanar a Minna

Ƴansanda sun kama ƙarin mutum 24 kan zanga-zangar da aka gudanar a Minna



Rundunar ƴansanda Najeriya ta tabbatar da kama Aisha Jibril, wacce ta jagoranci zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Minna a Litinin da ta gabata. Bayan kama Aisha, rundunar ta kama ƙarin mutane 24.

A'isha, ta jagoranci gudanar da zanga-zanga a birnin Minna, inda suka toshe babban titin Minna-Bada, da shataletalen Kpakungu, suna neman gwamnati ka kawo karshen tsadar rayuwa a Najeriya.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, cikin sakon da ya fitar a yau Laraba, ya tabbatar da kama Aisha da karin wasu mutane, inda ya ce zasu gurfanar dasu a gaban kuliya.


Post a Comment

0 Comments