Auren Mace masifaffiya yanada matukar fa'ida da anfani inji malam Aminu Daurawa.

 Auren Mace masifaffiya yanada matukar fa'ida da anfani inji malam Aminu Daurawa.    

  


Shugaban hukumar Hizba ta jihar Kano sheikh Aminu Daurawa ya fada cewa  auren mace masifaffiya yanada anfani sosan gaske (ya Fadi Hakanne a cikin raha) domin zai taimakeka wajen komawa Mai yawan ambaton Allah a koda yaushe.   

Sannan idan kanada kiba masifar ta kadai zai ramar da Kai.  

Haka zalika zata sa ka dinga fita kasuwa da wuri kuma bazaka dawo gida ba sai tattalin Arzikin Ka ya yawaita ko aikin office kake bazaka makara ba.

Zata saka Ka daina kallon matan mutane, sannan masifar zata saka kullum kana goge goge a wayar Ka, kaga ka Zama mai tsoron Allah.

Zata saka Ka koma yin biyayya ga mahaifiyar Ka.

Zata koya maka tsayuwar dare kana gayama Allah.

Za'a Dunga kankare Maka zunubi saboda masifarta.


Shin zaku iya fatan Allah ya Baku mace masifaffiya?

Post a Comment

0 Comments