Biden ya lashe zaɓen fitar da gwani a jihar South Carolina

Biden ya lashe zaɓen fitar da gwani a jihar South Carolina



Shugaban Amurka Joe Biden ya samu gagarumar nasara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar Democrats a jihar South Carolina.


Yayin da aka ƙirga kusan duka ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen na ranar Asabar, mista Biden ya samu ƙuri'un duka wakilai 55, kamar yadda kafar yaɗa labaran CBS ta Amurka ta bayyana.


Wannan shi ne zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar Democrat na farko, gabanin zaɓen shugaban ƙasar da za a yi cikin wannan shekara.


Shugaba Biden - wanda ba ya fuskantar hamayya mai yawa a cikin jam'iyyarsa - ya yi alƙawarin kayar da tsohon ƙasar, Donald Trump na jam'iyyar Republican.


Mista Biden ya tuna yadda masu kaɗa kuri'a a South Carolina suka "taimaki takararsa'' a 2020.


Shugaban na Amurka ya kuma ce "ba shi da shakku" za su dora shi kan hanyar lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2024.

Post a Comment

0 Comments