CBN zata dawo da siyar da Dala ga BDC's

 CBN zata dawo da siyar da Dala ga BDC's


Daga Na yartalla

Circular ta fita daga CBN kan cewa Bankin zai dawo da tsarin siyarwa da BDC's Dollar 💵 akan farashin N1, 301 kowace Dollar 💵 ɗaya. Su kuma an yarje musu su siyar da ita kan ƙarin ribar da bai wuce kaso ɗaya na jimillar farashin CBN ba. 

Bankin ya tsaurara matakai masu ƙarfin gaske, wanda karya su na iya janyo salwantar lasisin kamfanin BDC ɗin.

A cikin dokokin, wajibi ne kamfanin ya samar da rijista wacce za ta bayyana waƴanda suka siyarwa da Dollar 💵 da kuma adadin da suka siyar musu a kowace rana.

Dole ne kamfanin ya kiyaye ƙetare iyakar adadin da doka ta yarjewa mai siyan Dollar 💵 a tsarin PTA na kar ya haura Dollar 💵 dubu 4. Mai BTA kuma kar ya haura Dollar 💵 dubu 5. Ƙetare hakan saɓawa doka ne. Kuma kaso 25 ne kawai zai zamanto cash, ragowar kaso 75 kuma zai kasance electronically. 

Wajibi ne kamfanin ya ringa tura rahoton hada-hadar da yayi ta portal ɗin da CBN ya tanada kafin ko kuma ƙarfe 10 na safiyar washe-garin ranar da ta gabata.

Kamfanin ba zai taɓa siyar da Dollar 💵 haka nan kawai ba har sai da cikakkiyar shaidar dalilin da ya janyo buƙatar siyan nata. Wanda bayanin dalilin zai kasance ƙunshe cikin rijistar waƴanda aka siyarwa da take ƙunshe da dukkannin bayanan su.

Kasuwar tsaye ta haramta. Dole ne kamfani yayi hada-hadar kasuwancin sa a address ɗin da yayi rijista, wanda CBN ta sani. Kuma dole ne ya saƙale allon dake ɗauke da farashi a offishin.

Hukunci ne mai tsaurin gaske ga duk wanda aka kama a kan titi yana hada-hadar Dollar 💵. Domin an baiwa dukkannin hukumomin tsaro umarni da hukumomin EFCC da ICPC da NFIU su sanya idanu.

Da wannan tsarin da aka fitar kafin tabbatar da babban tsarin da zai sauya fasalin kasuwancin BDC's, babu shakka Bankin CBN gyara ya nufa. Kuma muna fatan alkhairi tare da nuna goyon baya.

Kar ku tambayeni ta yaya za a baiwa BDC's Dollar 💵 akan farashin N1,301, domin a halin yanzu ban san mecece madogarar Bankin ba.

Post a Comment

0 Comments