Dubun masu garkuwa da Mutane ta cika a Abuja

Dubun masu garkuwa da Mutane ta cika a Abuja



An Kama Masu Garkuwa Da Mutane Dauke Da Kudin Fansa Naira Milyan Tara

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta kama wasu mashahuran masu garkuwa da mutane a Abuja, inda aka samu naira milyan tara a hannunsu cikin kudin fansa da suka karba. 

An kama su ne a yankunan Tudun Wada Lugbe da Pyakasa unguwar Trademore a cikin Abuja.

Wadanda aka kama sune;

1. Usman Muazu, Kwali, FCT

2. Aliyu Mohammed, jihar Borno

3. Awwal Dahiru, Gwagwalada FCT

4. Rabi Sani, Safana, Katsina

5. Madina Abubakar, Niger state

6. Yunusa Elimelek, Kaduna

7. Saminu Idris, Kauru, Kaduna

8. Mariji Iliya, Mangu, Plateau

Post a Comment

0 Comments