Gwamnatin Nijeriya za ta daina biyan tallafi kan lantarki - Minista Adebayo

Gwamnatin Nijeriya za ta daina biyan tallafi kan lantarki  - Minista Adebayo



Ministan Lantarki na Nijeriya Adebayo Adelabu ya ce ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki na, yana mai cewa dole ne Nijeriya ta fara komawa kan tsarin kudin fito mai inganci, domin a halin yanzu kamfanonin da ke samar da wutar lantarki (GenCos) na bin kasar bashin Naira tiriliyan 1.3 da kuma kamfanonin iskar gas masu bin ta bashin dala biliyan 1.3.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka yi a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce Naira biliyan 450 ne kawai aka ware domin tallafin lantarki a bana amma ma’aikatarsa na bukatar sama da naira tiriliyan biyu domin biyan tallafin.

Tun a farkon wannan watan na Fabrairu ne aka rawaito ministan yana jaddada batun cewa ya kamata a cire tallafin lantarki a Nijeriyar, yana mai cewa a shekarar 2023 da ta gabata gwamnatin tarayya ta kashe naira biliyan 700 a biyan tallafin mai.

Batun da ministan ya yi a makon da ya wuce ya jawo mayar da martani daga mafi yawan ƴan ƙasar da ke nuna adawa da hakan.

Ko a ranar Litinin ma Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF ya buƙaci Nijeriya ta cire tallafin lantarki da na man fetur baki ɗaya, a matsayin wani ɓangare na matakan magance matsololin tattalin arziki da ƙasar ke fustanta.

IMF ta faɗi hakan ne a wani rahoto da ta fitar bayan kammala nazari kan sha'anin kudi na Nijeriya. IMF ta ce hakan ya zama wajibi ne saboda tallafin baya isa ga waɗanda ake son su amfana da shi.

Ya ce a yanzu za a bar gwamnatocin jihohi su riƙa samar da wutar lantarki ba tare da kashin kansu ba don samar da wutar lantarki ga jihohinsu.

Da yake magana a kan tashar da ta durkushe kusan sau shida tsakanin watan Disambar 2023 zuwa yanzu, ya ce hakan ya faru ne sakamakon karancin iskar gas da tsufa injina da karancin karfin wutar lantarki da aka samu, da lalata tashoshin wutar lantarki a wasu sassan kasar.

Channels TV ta rawaito ministan a wajen taron yana ƙarawa da cewa Kamfanin da ke isar da wutar ga yankuna a fadin kasar yana da ayyuka sama da 100 da aka yi watsi da su saboda bambancin alkaluman kwangilolin da ake samu a sakamakon tashin farashin kayayyaki, don haka kamfanin ba zai ba da wasau sabbin kwangiloli ba har sai an kammala duk irin wadannan ayyuka.

Ministan ya kuma ce an ware sama da Naira biliyan 50 a kasafin kudin shekarar 2024 domin gina kananan cibiyoyin samar da wutar lantarki ga lunguna da saƙo-saƙo na ƙasar.

Post a Comment

0 Comments