Gwamnatin Nijeriya za ta fara kayyade farashin kayan masarufi

Gwamnatin Nijeriya za ta fara kayyade farashin kayan masarufi

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.

Tuni aka soma zanga-zanga a wasu sassan ƙasar sakamakon hauhawar farashin kayan abinci.

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirinta na kafa kwamitin ƙayyade farashin kayan abinci.

Mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima ne ya sanar da hakan a ranar Talata a lokacin wani taron kwana biyu kan batun sauyin yanayi da abinci.

Shettima ya ce za a ɗauki wannan matakin ne a yunƙurin daƙile hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

A sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar, ta ce kwamitin zai mayar da hankali wajen kula da daidaita farashin abinci.

Sai dai a sanarwar, gwamnatin ba ta bayyana ainahin lokacin da za ta kafa wannan kwamitin ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsaloli na tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar.


Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ta jawo zanga-zanga a wasu sassan ƙasar waɗanda suka haɗa da Neja da Kano.


Sai dai gwamnatin ƙasar ta ce tana iya ƙoƙarinta wurin ganin ta shawo kan matsalar inda ɗaya daga cikin matakan da ta ɗauka har da na bayar da umarnin fitar da dubban buhunan hatsi daga baitul-malin ƙasar domin rage yunwa a ƙasar.

Post a Comment

0 Comments