Haihuwar shugaban samarin Aljanna imamu Alhusain jikan manzon Allah (S)

Haihuwar shugaban samarin Aljanna imamu Alhusain jikan manzon Allah (S)


Daga Jawad Adamu Tsoho 

A irin wannan rana ta 3 Ga Watan Sha'aban, a Shekara ta 4 bayan Hijira aka Haifi Imam Hussain Shugaban Samarin Aljanna ,Wato Imami na 3 a cikin Jerin Limaman Shiriya. 

An Haifi Imam Hussain (As) ne a ranar Alhamis, 3 ga Sha'aban Shekara ta 4 bayan Hijira. Wato 10 January 626 Miladiyya. 

Mahaifinsa Shine Amirul Muminin Ali bin Abi Talib,Mahaifiyarsa Kuma Itace Yar Manzon Allah (S) Sayyida Fatima (As) wacce itace Shugaban Matan Duniya da Lahira.

Imam Hussain (As) Yanada Lakabobi Masu Yawa daga ciki sune: Sibtis Sani,Sayyidus Shuhada, Imamus Salis, Ash-Shahidu Bi Karbala,Dalil Ala Zatillah.

Amma Anfi Saninsa da Aba Abdullah Wanda Shine Alkunyarsa.

Bayan Yiwa Manzon Allah Albishir da Haihuwar Imam Hussain (As) a wannan lokacin Manzon Allah Ya Tafi gidan Imam Ali (As) Ya Umurci Asma'u Bintu Umais data Kawo Masa Imam Hussain (As) ,Bayan ta kawoshi dauke a cikin farin Zani. Sai Annabi Yayi Murna yayi farin ciki da ganin Al Imamu Husain (As) Ya rungumeshi, Ya kira Sallah a Kunnensa na dama, Ya Kuma yi Ikama a kunnensa na Hagu, Sannan Ya dora shi a Kan Cinyarsa Mai Albarka nan take akaga Manzon Allah Yana kuka, Sai Asma'u cikin Mamaki take Tambayar Shi Ya Rasulullah (S) Shin Wa Kake Yiwa Kuka ? Manzon Allah Yace Dan nan nawa nake Yiwa Kuka, Asma'u tace Ya Rasulullah Yanzu fa aka Haifesa! Sai Manzon Ya Amsa mata da cewa Ya Asma'u Akwai Wata Azzalumar Kungiya Karkatacciya sa zata Kashe shi a bayana. Allah ba zai hada su da Cetona ba, Sannan sai Yace Ya Asma'u Karki Fadawa Yata Fatima wannan Labarin Domin bata dade da Haihuwar saba.

Sai Manzon Allah (S) Ya Sami Sako daga Allah Game da sunan Abin Haihuwarsa Mai daraja, Sai Annabi Yace wa Imam Ali Ka sa Masa suna Hussain. 

An samo daga Imamu as-Sadiq (As) Yace: "Wata rana wasu gungu na Sahabbai Sun je wajen Manzon Allah (S) domin Su taya Shi murnar haihuwar Imamu Husain (As), sai daya daga cikin Shabban ya ce: Ya rasulallah, mun fa ga abin al'ajabi dangane da Ali Dan Abi Dalib!.

Sai Ma'aiki (S) Yace: "Me ku ka gani ne dangane da Shi"?

Sai Suka ce: Mun zo ne mu gaishe Ka kuma Mu taya Ka murnar haihuwar Husain, sai Ali ya hana mu shigowa, da muka tambaye Shi dalili, sai yace da Mu: Ai Ka yi bakin Mala'iku ne su dubu dari da dubu ashirin da hudu!. Shi ne mamaki ya kama mu!, kan ya aka yi ya san adadin Mala'ikun da Suka zo wajen ka!

Sai Ma'aiki (S) ya kalli Ali ya yi murmushi yace:"Ya Ali, wa ya sanar da Kai cewa Mala'iku dubu dari da dubu ashirin da hudu Sun zo waje na? 

Sai Yace: Mahaifana Su zama fansar Ka ya Rasulallah! na ji sautin Mala'iku ne tare da Kai, kuma na ji Suna magana ne da Yarurruka daban-daban har yare dubu dari da dubu ashirin da hudu, sai na fahimci cewa lallai Mala'ikun Su dubu dari da dubu ashirin da hudu ne.

 Sai Ma'aiki (S) yace da Shi: "Allah ya kara maka ilimi da hakuri ya Baban Hasan".

Littafin Manakibu ali abi Dalib, juzu'i na 2 shafi na 55.

Tabbas Imam Hussain Yanada Babban Matsayi na daban. Bayan Ayoyin Alkur'ani da suka Ambacesa a cikin Ahlulbait (As) kamar Ayar Tsarkakewa (Ayatut-Tathir) Ayar Tsarkakewa, Ayar Mubahala, Ayar Kauna (Ayatul Mawadda). Bangaren Hadisi Kuma akwai Hadisan Manzon Allah Masu Girma da Matsayinsa da daukakarsa da Kuma Darajarsa. Daga cikin su:

An ruwaito daga Salman al-Farisi, ya ce: na ji Manzon Allah(saw) yana cewa: "Hasan da Husaini 'ya'yana ne, wanda ya so su ya so ni, wanda kuma ya so ni; Allah zai so shi, wanda kuwa Allah Ya so zai shigar da shi Al-jannah. Kuma wanda ya fusata su ya fusata ni, wanda kuma ya fusata ni Allah zai yi fushi da shi, wanda kuwa Allah Ya yi fushi da shi zai shigar da shi wuta". (A'alam al-Warah, shafi na 219).

Magana Akan Dabi'un Imam Husain(As) kuwa ba abu bane me sauki domin Hakika kasantuwan Imam Hussain (As) ya tashi ne karkashin kulawar kakansa Manzo(S), babansa Ali(As) da mahaifiyarsa al-Zahara(As), ta sa dabi'unsa na misalta sakon Allah(t) a nazarce, aikace da halayya.

Shu'aib bin Abdul-Rahman ya ruwaito cewa: "An ga wani tabo a bayan Imam Husain(As) a Karbala; sai aka tambayi Imam Zainul-Abidin(As) game da shi, sai ya amsa da cewa: "Wannan ya samo asali ne daga buhunan abinci da yake dauka a bayansa yana kai wa gidajen matan da mazansu suka mutu da marayu da miskinai ".

Amincin Allah Ya Cigaba Da a Gareka Ranar da Aka Haifeka da Ranar da Zaka Tashi Kana Mazlumi Wanda Aka Zalunta tare da Iyalan Gidanka Tsarkaka❤.


 Jawad Adamu Tsoho 

Post a Comment

0 Comments