Harkar musulunci ƙarƙashin Sheikh Zakzaky sun gudanar da taron Tunawa da shahidai karo na 33 a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja

Harkar musulunci ƙarƙashin Sheikh  Zakzaky  sun gudanar da taron Tunawa da shahidai karo na 33 a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja.



A Safiyar Ranar Lahadi 4 ga watan Fabarairu shekerar 2024, cincirindo yan uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) suka yi taro a filin taro na City park dake kan titin Ahmad Bello way dake yankin Wuse 2 domin gudanar da taron Tunawa da shahidan da aka kashe ma Yan gwagwarmayar, an fara gudanar da taron da addu'a daga bakin Sheikh Sidi Muneer, Sannan Yan Intizar suka gudanar da Karatun Alƙur'an mai girma, sannan aka ba Mawaka filin suna Waƙoƙin jinjina ga Shahidai ana Zagayawa da hotunan Shahidai, bayan kammala wannan ne daya daga cikin iyalan Shahidai Ya Karanta Ziyarar Imam Musal Kazeem (a.s) sannan wasu daga cikin Iyayen Shahidai suka gudanar da Jawabai akan Rayuwar ƴaƴansu da suka yi shahada, bayan sun kammala ne Shugabar Mu'assatu Shuhada.

Malama Maryam Gashua ce ta gabatar da Jawabi, a cikin Jawabin na ta tayi kira ga yan uwa akan Muhimmatar da biyan Haƙƙin Shahidan  tare da gabatar da sabon na'urar biyan Haƙƙin Shuhada, wanda zai ba da damar da mutun ya biya kai tsaye kuɗin ke tafiya ga asusun Mu'assasar, bayan kammala Jawabin na tane aka gabatar da Jawabin mai gayya mai aiki kuma Jagoran tafiyar Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) inda Jagora (H) ya gabatar da Jawabai mai Ratsa zukata, tare da kawo tarihin shahadar Imam Musal Kazeem, sannan daga bisani yayi Nasiha ga yan uwa tare da jan hankalin masu aukar da Shahadar, daga ƙarshe Jagora yayi albishir ga yan uwa, akan lallai akwai ranar Ɗaukar fansa akwai ranar darawa.




Post a Comment

0 Comments