Hukumar FCCPC ta garkame Sahad Stores

Hukumar FCCPC ta garkame Sahad Stores



Hukumar Kula da Kare Hakkin Masu Saye da Sayarwa ta Nijeriya, (FCCPC) ta rufe ɗaya daga cikin manyan kantunan sayar da kayan masarufi na Sahad Stores da ke Abuja, wanda yake unguwar Garki.

Hukumar ta zargi kantin da tsauwala wa masu saye ta hanyar sauya farashi idan suka zo biyan kuɗi daga ainihin farashin da aka saka a jikin kayan da ke kan kantoci.

Lamarin na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shirinsa na ɗaukar matakan daƙile matsalar abinci da ake fama da ita a ƙasar.

Muƙaddashin shugaban hukumar FCCPC Adamu Ahmed Abdullahi ne ya jagoranci tawagar da ta je rufe kantin.

Adamu Abdullahi ya shaida wa ƴan jarida cewa binciken farko-farko ya tabbatar da cewa hukumar kantin tana tsauwala wa masu sayayya a lokacin da suka zo biyan kudi.

"Abin da muka gano a tattare da waɗannan mutane shi ne rashin gaskiya wajen ƙayyade farashin kayayyakinsu, wanda hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulki sashe na 115, sakin layi na 3, wacce ta ce bai kamata mai sayayya ya biya kuɗin kaya da ya zarce wanda ya gani an rubuta a jikin kayan ba," a cewar Adamu Abdullahi.

FCCPC ta ce kantin zai ci gaba da kasancewa a kulle har sai an kammala bincike.

Post a Comment

0 Comments