Hukumar Hizba ta jihar kano tayi nasarar kama murja kunya

Hukumar Hizba ta jihar kano tayi nasarar kama murja kunya.



Bayan Jan kunne da rarrashi Hadi da tsawatarwa  da  hukumar Hizba takewa Murja amma ta sa kafa ta Shure, abun nata sai karuwa yake har ta soma kawo bakin Yan Daudu daga Makita. Yanzu haka Hukumar Hisba ta cafketa kallo ya koma Sama.

A baya ma gwamnatin Ganduje ta kaita gaban kuliya inda a ka tabbatar da tana da cikakken hankali Amma alkali yayi Mata sassaucin kukunci na sharar asibiti tare da alkawarin bazata sake aikata laifin da takeba Amman yanzu tayi kunnan uwar shegu ta kuma aikata laifin da yafi na Baya.



Post a Comment

0 Comments