Hukumar NDLEA ta kama wani mutum da ya ke kaiwa ‘yan ta’adda kwayoyi.

 Hukumar NDLEA ta kama wani mutum da ya ke kaiwa ‘yan ta’adda kwayoyi.



Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 42 mai suna Ahmad Mohammed da ke da alhakin kai wa masu tayar da kayar baya magunguna a jihar Borno. 

A wata sanarwa da Daraktan yada labarai na hukumar Femi Babafemi ya fitar ranar Lahadi, wanda ake zargin yana cikin kashi 24 da ake zargi da fataucin mutane da dillalai da jami’an ta suka kama kwanan nan. 

Sanarwar ta bayyana cewa Mohammed yana ba wa masu tada kayar baya miyagun kwayoyi a Bakin iyaka da Najeriya da Kamaru.

Jami’an NDLEA sun kama shi ne a ranar Juma’a 9 ga watan Fabrairu a shingen bincike a jihar Borno. Sanarwar ta ce "Lokacin da aka binciko kayansa kwalayen tramadol guda 20,000 aka kwace daga hannunsa yayin da yake kan hanyarsa ta kai kayan a garin kan iyaka." 

A wani labarin kuma, jami’an hukumar NDLEA da ke aiki da sahihan bayanan sirri a ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairu sun kama wata mota kirar Legas JJJ 64 YC dauke da buhunan tabar wiwi guda 367 mai nauyin kilogiram 4,037 daga Akure, jihar Ondo wanda za a kai a unguwar Shabu da ke Lafia babban birnin jihar. 

Mutane uku da ake zargi sune Shuaibu Yahaya Liman, 35; sai Monday Audu mai shekaru 33 da kuma Linus Samuel mai shekaru 42 da dukansu an samu nasarar kama su.

Post a Comment

0 Comments