Hukumar tsaro ta farin Kaya tayi nasarar kama wani ma'aikacin civil defence dake safarar makamai da harsasai ba bisa ka'ida ba.

 Hukumar tsaro ta farin Kaya tayi nasarar kama wani ma'aikacin civil defence dake safarar makamai da harsasai ba bisa ka'ida ba.



Daga Ismail Mohammad Goje

Hukumar Tsaro ta farin kaya tayi Nasarar bin wani Civil Defense mai mukamin ASC Idris Sa'idu tareda kama shi da makamai da harsasai a Kauyen Fadikpe dake Karamar Hukumar Chanchanga na Jihar Niger inda yake safarar su ba bisa Ka'ida ba daga gari zuwa wajen Gari ma Yan Ta'adda da suke ta da garuruwan Mutane a Arewacin Najeriya.

ASC Idris Sa'idu Mutumin Kauyen Maje ne na Karamar Hukumar Lapai dake Jihar Niger. Shi dai ASC Idris Sa'idu Ma'aikaci ne a Hukumar Civil Defense na Najeriya, wanda ya amsa laifin da ake tuhumar sa dashi. A yanzu haka yana karkashin kulawar sashin Bincike na Fikira domin tasan wasu bayanai.

Ubangiji ya kawo mana Karshen Ta'addancin da yake damun mu a wannan Kasa tamu Najeriya, musamman Arewa. Allah duk kai Hannu a Matsalar Tsaro kayi mana maganin sa, ka tona masa Asiri, ka Gigita shi. Ameen ya Rabbi!!!


Post a Comment

0 Comments