"Ina da muhimman dubarun da zan yi don samun isasshen abinci ga kasa" Tinubu

 Tinubu ya yi wa yan Nijeriya albishir mai daɗi da sa su farin ciki inda ya ce "Ina da muhimman dubarun da zan yi don samun isasshen abinci ga kasa"



Shugaban kasa Tinubu ya bayyana cewa yana da muhimman abubuwan da zai yi a gwamnatinsa don samar da isashen abinci a kasar ta hanyar bunkasa noma

Shugaban ya faɗi yakan ne a lokacin da tawagar shuwagabannin Ɗarikar Tijjaniyya suka kai masa ziyara a fadarsa dake Aso Villa 

Ya ce daga cikin hanyoyin da zai bi don magance matsalar abinci a kasar nan shi ne, zai kara samar da kasar noma, sannan zai tallafa wa manoma da basuka masu ƙarancin ruwa don su fadada sana'arsu ta noma abinci ya wadaci kasa ko'ina

Post a Comment

0 Comments