Isra'ila ta saki Falasdinawa 114, mafi yawansu sun samu karaya.
Hukumomin Isra'ila sun saki Falasdinawa 114 da suka hada da mata hudu da sojojin Isra'ila suka tsare a lokacin farmakin da suka kai a Zirin Gaza a baya-bayan nan.
Wani jami'in Falasdinawa da ke kula da mashigar Gaza ya bayyana cewa, an sako Falasdinawan ta hanyar mashigar kasuwanci ta Karem Abu Salem, wacce aka fi sani da Mashigar Kerem Shalom, a kudancin Gaza.
An kai goma daga cikin mutanen da aka sako ciki har da wata mata zuwa asibiti a birnin Rafah saboda yanayin lafiya.
Wata majiyar lafiya ta ce sun sami karaya mai muni musamman a hannayensu da kafafunsu, sakamakon dukan da sojojin Isra'ila suka yi musu a hannunsu.
Wasu sun samu toshewar jini a wuyansu da kawunansu, yayin da wasu kuma ke fama da wahalar numfashi da raunuka da sagewa da kumburin hannayensu, in ji majiyar.
0 Comments