Jagoran harkar musulunci a Najeriya sheikh Zakzaky ya dawo daga jinya daga kasar Iran.

 Jagoran harkar musulunci a Najeriya sheikh Zakzaky ya dawo daga jinya daga kasar Iran.



Daga Mahadi Umar kaita

Jagora Sheikh Zakzaky tare da Mai dakinsa malama zenatudden Ibraheem Zakzaky sun dawo daga jinyar da sukaje a jamhuriyar Musulunci ta kasar iran, jagoran Wanda suka dauki tsawon lokachi a tafiya jinyar da sukai.

Shafin office din jagoran ne ya wallafa haka a Daren jiya inda ya bayyana an samu ci gaba sosai shehin malamin sun dawo lafiya daga tafiya jinyar, inda office din ya bayyana ranar Laraba, 11 Sha'aban, 1445 (21 Fabrairu, 2024) a matsayin ranar da za'ayi bikin murna da dawowar tashi a babban birnin tarayya dake Abuja.

Wakilinmu ya samu Jin ta bakin Daya daga cikin Almajiran malamin inda ya bayyanawa wakilin namu matukar jin dadinsu inda yace "zamuyi kokari wajen ganin mun cika babban birnin tarayya domin nuna soyayyarmu ga Jagoranmu.


Ku kasance damu domin Jin rahoton yacce taron zai kasance kai tsaye a shafukanmu na sada zumuta.


Post a Comment

0 Comments