Jami'an tsaro sakai sun Samu Nasarar Kwato Wasu Mutum Biyar daga Hannun Ƴan'tadda a Ƙaramar hukumar Batsari.

Jami'an tsaro sakai sun Samu Nasarar Kwato Wasu Mutum Biyar daga Hannun Ƴan'tadda a Ƙaramar hukumar Batsari.



Jami'an Tsaron Katsina Community Watch Corps Sun ƙara Samun Nasarar Kwato Wasu Mutum Biyar daga Hannun Ƴan'tadda a Ƙaramar hukumar Batsari.

Ƴan'taddan Dai Sun Kama Waɗannan Mutane Ne a Yammacin Batsarin Jahar Katsina Inda suka Karɓi Kuɗin Fansa kuma Suka ƙi Sakin Su.

Cikin Ikon Allah Jami'an Tsaron da Mai Girma Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda Ya Assasa Wato Katsina Community Watch Corps Sun Tunkari Mafakar Waɗannan ɓarayi Kuma Allah Ya basu Nasarar Karɓosu Cikin Aminci.

Falalu Lawal Katsina

Media Assistant to The Katsina State Governor Ministery Of Internal Security and Home Affairs

12/02/2024.

Post a Comment

0 Comments