KAI TSAYE: Daga Mashood Abiola Stadium Yanzu Haka Ana Shirye-shiryen fara taron Tarbar Sheikh Zakzaky

 KAI TSAYE: Daga Mashood Abiola Stadium Yanzu Haka Ana Shirye-shiryen fara taron Tarbar Sheikh Zakzaky 



Daga Mahadi Umar kaita

Tun Daren jiya Talata 20 ga watan February nan da muke ciki birnin Abuja ya dauki harama ya cika fal duk inda Ka duba babu abunda kake gani sai dandazo jama'a masoya da mabiya na sheikh Zakzaky wadanda suka zo birnin tarayyar domin tarbar Sheikh din.

Taron dai Wanda za'a gudanar a Mashood Abiola Stadium ana kyautata zaton zai kwashi tandazon jama'a maras adadi duba ga yawan mabiyan shehun malamin sannan Kuma ga shaukin ganinshi da akeyi dukda babu tabbacin zai halarci wajen taron,  Amman saboda tsantsar sallamawa gami da sadaukarwar mabiyan nashi basuyi kasa a gwiwa ba sun halarci taron.

Ana kyautata zaton taron zai Tara mahalarta Sama da mutum  miliyan Daya Wanda ba'a ta6a kamarsa ba tun bayan da gwamnatin Buhari ta afkawa mabiyan nashi a 12/12/2015 a Husainiyya Baqiyatullah da gidansa dake Gyallesu Zaria dama wasu muhallin mallakin sheikh din da mabiyansa a cikin garin zaria jihar Kaduna.

Ana kyautata zaton sheikh Zakzaky zai bayyana a gaban miliyoyin mabiyanshi Kuma idan Hakan ya kasance tohm wannan itace bayyanar Shi a bainar jama'a ta farko tun bayan da aka saki sheikh din daga daurin zaluncin da kasar tayi mashi.

Ku biyo mu domin Jin cikakken rahoto Akan wannan gagarumin taron Wanda ake shirin gudanarwa yanzu haka.


Ku kasance da MURYAR LABARAI


Post a Comment

0 Comments