Mahdawiyyah a fikirar gwagwarmaya Kashi na 1

 Mahdawiyyah a fikirar gwagwarmaya Kashi na 1



Gabatarwa

Mahdawiyyah, Mahdism yana daga cikin tunanunnukan da suka hada mutanen Duniya gaba-daya, Musulmansu da sauran addinai da suke anbata samuwar mai ceto a karshen Zamani, kowanne bagare na al'umma suna da fuskar da suka fahimci wannan al'amari, sai dai a fuska mafi muhimmanci da tushe na asali wadda take ayyana wannan mai ceton a suna da alamomi hade da abubuwan da suka kebance shi, ya zama ana da karancin Masaniya. Amma su Shi'a sun san shi ta wannan fuskar saboda tarihinsa da suke da shi ta hanyar hadisai karbabbu kuma tabbatattu a wajensu.

Kallon Mahdawiyyah a matsayin wani bayyanannen al'amari a duniyar Shi'a, ya samar da fifiko a gare su a wannan al'amari, domin a wurin su ba wai tunani ne na fata ba, sai dai matsayin Hujjar Allah, rayayye a cikin mutane, yana ta'ammuli da mutane a matsayin Jagora, da dukkan hujjojin da suke zaunar musu da imanin hakan. A duniyar musulunci, wadanda ba su karbi wannan akidar ba, basu iya kawo dalili na hankali da zai iya kore wannan fikirar, wanda wasu dalilan da suka tabbatar da samuwar wannan shugaba yawancin su suna gaskata su a ruwayoyinsu mabanbanta.

 Shaheed Ahmad Zakzaky (H) ya tarbiyyantu a cikin wannan Fikira, ta fuskar da dukkan wani tunani da ayyukansa sun ginu ne a tattare da wannan al'amari. Fahimtar Mahdawiyyah zai taimake mu wajen fahimtar irin abunda yake hange, da amsa kiran da yayi gare mu daga sakonsa na farkarwa._


Sigh:- Jasaz, Aza Department Mngnt Board

Post a Comment

0 Comments