Mahdawiyyah a fikirar gwagwarmaya Kashi na biyu


Mahdawiyyah a fikirar gwagwarmaya Kashi na biyu 



Wannan rubutun zai Dunga zuwa maku a lokaci bayan lokaci.

Fahimtar Mahdawiyyah da Intizarul Faraj._


Imam Mahdi, dan Imam Hassan Al-Askari (AS), mai tsarki da albarka, an san tarihin haihuwar sa, su waye iyayensa da sahabbansa wadanda suka kasance wakilansa a Gaiba qarama (Sugra). A cikin mu'ujizozin sa, Allah ya bashi tsawon rai, bai gushe ba har yanzu yana cikin al'ummun duniya a gangar jiki, wanda kuma shine fatan dukkan al'ummah (wannan shine abinda Shi'a suka kebanta dashi dangane da wannan muhimmin al'amari.

Shaheed Ahmad Zakzaky yayi kokarin fahimtar damu wasu al'amura da suke ginshikai a cikin wannan al'amari da zai sanya saninmu da wannan shugaba da al'amarinsa zai tashi daga fata kadai, zuwa ga aiki mai rayar da wannan fatan.


Fahimtar cewa, samuwar wannan Shugaba Al-Imamul Mahdi (AF) cigaba ne na jerin masu da'awa zuwa ga Allah, wanda Allah (SWT) ya saka su daga farkon tarihi har zuwa yau, cikin Annabawa da Manzannin sa har zuwa ga cikamakon Annabawa (SAWW), har lamarin ya kai ga Imamin zamanin nan (AJTF), dukkaninsu jerin silsila ne mai hadewa da juna a tarihin 'yan Adam. Sanin hakan zai nusar da mu fahimtar cewa wannan igiyar tana shiryatarwa zuwa ga Allah da annabta bata yan keba har a wannan zamanin, domin hujjar hankali ta nuna buqatuwar Dan-Adam ga shiryatarwa na annabawa da Manzanni cikin salon da'awa zuwa ga Allah. Mu sani, irin tarbiyyan da Annabawa sukai ta bayarwa ga Dan-Adam ta wanzu a tunanin Shaheed Ahmad da mu'amalarsa, zamani yana nisa mutane na kara kusa da koyarwar da ake ginawa.

Mutane a yau, sanadiyyar cigaba na tunani, ilimi da wayewan zamani da ya karu a wannan al'umma, sun iya fahimtar da yawa daga karantarwar annabawa wanda ba zai yiwu mutanen baya su iya idrakin su a karnonin da suka gabata ba, kafin yanzu, lamarin adalci, 'yanci da girmama mutuncin Dan-Adam. Kalmomin da suke tashe a duniyar mu ta yau, sune Kalmomi da Zantukan Annabawa.


A wancan zamanonin, gama-garin mutane (Masses) basu iya fahimtar wadannan ma'ananonin sai dai bayan aiko musu da Annabawa da yaduwar da'awarsu, ta hakan wadannan fikirorin suka zaunu a kwakwalen su, har fidirar su da zantukansu suke sauyawa zuwa cigaba da fahimtar asasi na kamalar Mutuntaka. Silsilar masu da'awa zuwa ga Allah bata yanke a wannan zamanin ba, samuwar mai tsarki ta Baqiyyatullahil-A'azam shine cigaban wannan da'awar mai saita Dan-Adam zuwa ga Kamala. Kamar yadda muke karantawa a Ziyarar Ali-Yasin... "Assalamu alaika ya da'iyallah wa rabbaniyyah ayatihi..." a yau muna fahimtar cewa shi Imam shine Ruhi da gangar jiki da ke wanzar da da'awar Annabi Ibrahim, Annabi Musa, Annabi Isah da dukkan annabawa har zuwa ga cikamakin su (SAWW). Duka ana ganin su da ayyukansu a tare da wannan babban Magajin nasu. Wanda bayyanarsa zai yi kira ga dukkan halittu na Allah, zai fito musu da ilimomi da koyarwar da Annabawa suka zo da shi tsawon zamani. Wannan shine asasin wilayar Allah (SWT) wadda Shaheed Ahmad Zakzaky (H) yayi kokarin farkar damu a kanta.


Sigh:- Jasaz, Aza Department Mngnt Board.

Post a Comment

0 Comments