Mahdawiyyah a fikirar gwagwarmaya Kashi na ukwu (3).

Mahdawiyyah a fikirar gwagwarmaya Kashi na ukwu (3).



Intizarul Faraj

 Intizarul faraj, Mafhum {Concept} ne mai fadin gaske; daya daga cikin ma'anoninsa shine 'Faraj' (Mafita) na karshe (Bayyanar Imam Mahdi). Yayin da mutane suke ganin Azzaluman duniya sun shagaltu da kwace da barna da shishshigi kan hakkokin mutane, kada su dauka shikenan wannan shine makomar duniya, kada ayi tunanin babu wani makawa sai mika wuya ga wannan yanayin. Intizarul Faraj na koyar da tunanin cewa wannan yanayin yanayi ne mai wucewa. Dukkan barna da za'ayi da zalunci da za'ayi wannan Concept din na fitar da mahangar wannan duniyar da makomarta shine hukunci ta adalci wadda tabbas za ta zo. Intizarul Faraj na da ma'anoni da yawa, wanda muka kawo misali ne daga ciki. 

A mafi karbabbiyar fahimta, wadda tayi dai-dai da hankali, yayin da muka ce muna jiran Faraj, wannan ba yana nufin faraj na karshe bane kawai. A'a, yana nufin kowacce tosashshiyar kofa zai yiwu a bude ta, wannan shine ma'anar Faraj:- budi. Musulmi a darasin Intizarul faraj yana koyon cewa babu wata hanya tosashshiya a rayuwar Dan-Adam da ba zai yiwu a bude ta ba, kuma be kamata a debe kauna a (Ya Fidda rai) sanyin gwiwa ya same shi, har yaji cewa ba zai iya yin komai ba. Domin idan har ya zama rayuwar mutane a karshen lamari a gaba da dukkan wannan zalunci da danniya akwai mafita, to hakan na nufin da akwai mafita da za'ayi tsammani ga dukkan shinge da shamaki na matsalolin da ke rayuwar mu a Yau. Wannan shine darasin fata ga dukkan Dan-Adam, kuma darasin Intizarul Faraj na hakika ga dukkan mutane. 

Shiyasa wannan Intizarul Faraj din ya zama mafi girman ibada a wannan Zamani, kamar yadda wannan al'umma ta zama mafificiya sabida Umarni da kyakyawa da hani ga mummuna. Kada mutum yayi kuskuren tunanin jira ne da za'a daure hannaye ayi ta jira har sai wani al'amari ya faru, Intizarul Faraj aiki ne da shiri mai samar da Kumaji da Hamasa a zuciya da zahiri. Aiki ne na Tajdidi a dukkan fagage. 

Da irin wannan tarbiyyah da shiri shine za'a gina al'ummar da ba zasu yanke fatan Faraj a wani lokaci daga lokuta ba. Jiran mafita na karshe, kamar yadda yake a jiran mafita a dukkan Marhalolin rayuwa na daidaiku da al'umma. Kada a bari cire tsammani da yankewar fata ya shiga zukata. A shiryawa al'amarin Faraj yadda zai zaunu a tunani da zukata ta yadda za'a gan shi tabbas zai tabbata, sai dai akwai sharadin jiran ya zama da gaske ake yinsa, akwai Aiki da Sa'ayi da Motsi a cikin sa. 

Lokacin da muke jiran Faraj da zai yi iko wajen tabbatar da adalci da rusa zaluncin da ya addabi rayuwar Dan-Adam, kamar yadda yake a buqatuwar duk wani farkakken mutum, wanda bai turbude furkarsa da son rai, ya nutse a kebantacciyar rayuwarsa (Individualist) ba. Kasancewarsa mutum da yake kallon rayuwar mutane a gaba-daya, dunkulalliyar kallo, toh tabbas zai kasance cikin yanayi na Intizar. Intizar na nufin kin gamsuwa da yarda da yanayin rayuwar da mutane ke ciki, da yin kokari wajen kaiwa ga yanayin da ake buqata, kuma abinda yake tabbatacce shine, wannan yanayin da ake buqata zai tabbata ne a hannun waliyin Allah, Hujjar sa dan Imam Hasaan, AlMahdi Sahubuz-Zaman (Salamullahi Alaihi). 

Idan har da gaske muna son kasancewa cikin masu Intizarul Faraj kamar yadda Shaheed Ahmad Zakzaky (H) yayi fatan mu kasance, dole mu shirya kanmu a matsayin Sojojin da a shirye suke don wancan yanayin, mu yi mujahada a wannan fagen. Intizarul-faraj ba yana nufin mutum ya zauna baya aikata komai ba, bai mike don wani gyara ba, da yunkurin samar da wani canji, sai dai kawai yana yiwa kansa fatan kasancewa cikin jerin masu Jiran Imamin Zamani (AJTF), wannan ba Intizar bane!

Menene Intizar? Intizar na nufin babu makawa Imam Mahdi zai bayyana cikin kudurar Allah (SWT), zai zo yayi anfani da wadannan mutanen da suka shirya don gamawa da ikon zalinci, da tabbatar da adalci a cikin mutane. Zai daga tutar Tauhidi a saman al'umma tayi iko. Shugaban da zai saka mutane su zama bayin Allah na hakika. Dole ne shiri don wannan al'amarin, duk wani motsi a hanyar tabbatar sa adalci yana a matsayin taku (step) zuwa ga wannan madaukakin hadafi. 

Sigh:- Jasaz, Aza Department Mngnt Board.

Post a Comment

0 Comments