Mashood Abiola Stadium ta gaza dauke dandazon al'ummar da sukazo tarbar sheikh Zakzaky

Mashood Abiola Stadium ta gaza  dauke dandazon al'ummar da sukazo tarbar sheikh Zakzaky

Dandazon jama'ar da basu sami Shiga cikin stadium din ba


Daga Mahadi Umar kaita

Babban Stadium din nan na kasa da kasa dake babban birnin Tarayyar Najeriya ya kasa dauke al'umman da sukazo domin tarbar Sheikh Zakzaky.

Inda stadium din ta cika makil da masoya da Yan uwa na Sheikh din duk inda Ka duba mutane ne kawai a cikin shauki da son ganin jagoran nasu.

Kasantuwar stadium din ba zai dauki yawan Al'ummar da tazo Wannan taron ba, Yanzu haka  Dubunnan daruruwan mutane ne basu samu shiga na suke a waje.


Ku biyo mu domin Jin yacce taron zai kasance Muryar Labarai




Post a Comment

0 Comments