Matsin Tattalin arziƙi da Najeriya ta ke ciki ba laifin Tinubu ba ne, -Sunusi Lamiɗo Sunusi
Mai martaba tsohon sarkin Kano, kana kuma tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi ya bayyana cewa bai yi adalci ba idan har ya fito ya ƙalubalanci shugaban ƙasa Tinubu kan matsayin tattalin arziƙin da Najeriya take ciki ba.
Ya ƙara da cewa an ɗora Najeriya ne a kan bashi shekaru takwas da suka gabata komai da aka yi an yi shi ne da kuɗin da aka aro.
Malam Lamiɗo ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabi ta bidiyon yanar gizo yayin wani bikin addini da aka gudanar a ranar Lahadi, inda ya ƙara da cewa duk ƴan Najeriya da suke son yayi magana a kan matsayin tattalin arziƙin da ƙasar take ciki to babu ko shakka suna buƙatar yayi adawa da shugaban ƙasa Tinubu ne.
Ya ƙara da cewa tun a baya ya bayyana matsayarsa game da munanan tsare-tsaren tattalin arziƙi da gwamnatin baya ta shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta aiwatar. Inda gwamnatin ta yi watsi da shawarwarin da ya bayar waɗanda za su taimakawa tattalin arziƙin.
Malam Sunusi ya ƙara da cewa duk wani masanin tattalin arziƙi wanda yake da cikakken hankali da tunani zai tabbatar da cewa tallafin man fetur da wannan gwamnati ta cire abu ne da ya dace wanda zai ceto Najeriya daga ƙangin bashi da gwamnatin baya ta jefa ta.
"Shekaru da dama na yi magana kan halin da za a iya samun kai na wannan matsin tattalin arziƙi da ake ciki. Duk wani masanin tattalin arziƙi da ya karanci tsare-tsaren harkar kuɗi na shekaru takwas baya ya san za a iya samun kai a wannan mummunan yanayi da ƴan ƙasa suka samu kai".
Malam Lamiɗo ya ƙara da cewa "wannan matsin da ake ciki somin-taɓi ne (idan har ba a ɗauki matakan da suka dace ba) domin kuwa Najeriya ita ma ƙasa ce kamar sauran ƙasashe; ƙasashe irin su Jamus, Zambabuwe, Uganda, da Benizuwela duk sun taɓa samun kansu a irin wannan yanayin.
"Gwamtin da ta gabata ta toshe kunnenta game da gyaran da muke bata kan (tsare-tsarenta na tattalin arziƙi). Na faɗi haka yayin wani zama a Jihar Kaduna. Duk wani ɗan siyasa da ya ce muku abubuwa za su yi sauƙi, ka da ku zaɓe shi domin ba gaskiya ya faɗa ba. Amma haka mutane suka yi watsi da shawarata suka siyasantar da ita". Ya ce.
"Idan har zan yi wa shugaban ƙasa Tinubu adalci, ba shi ne abin zargi kan matsin tattalin arziƙin da ake ciki ba; tsawon shekaru takwas muna rayuwar ƙarya da tarin bashi na cikin gida da ƙasashen ƙetare. Babban bankin ƙasa CBN ya biya sama da Naira Tiriliyan 30, wanda kaso ɗari bashi ne.
"Ni dai ba zan bi sahun ƴan Najeriya wajen ƙalubalantar shugaban ƙasa Tinubu kan wannan halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki ba. Ba wai na ce ba ya kuskure ba, amma dai a kan wannan hali na matsin tattalin arziƙi da ake ciki ba za a ɗora masa laifi ba. Zan yi magana idan har na ga wani tsarin tattalin arziƙi wanda kuskure ne nan gaba a gwamnatin Tinubu".
"Duk wanda ya ɗorawa Tinubu laifi kan wannan matsin tattalin arziƙi da ake ciki a yanzu bai yi masa adalci ba. Domin ba shi da wani zaɓi face ya cire tallafin man fetur. Ko da ma ba haka ba, Najeriya ba ta da ƙarfin da za ta iya cigaba da biyan tallafin man fetur". Ya ce.
"A shekaru takwas baya, babban bankin ƙasa, CBN, ya cigaba da buga takardun kuɗaɗe inda darajar Naira ta cigaba da karyewa. Akwai kuɗaɗe da yawa suna zagayawa a hannun mutane saboda babban bankin ƙasa ya buga kuɗaɗen batare da taƙaita yawansu ba". Ya ce.
"Tattalin arziƙin bai samu tsarin da ya kamata ba, sannan kuma ba sa ɗaukan shawara; a shekaru takwas ɗin da suka gabata, ba abin da suka assala, wasu shafaffu da mai na sayen dala a kan Naira 400 su sayar da ita Naira 600 zuwa Naira 700.
"Sai ka ga yaro wanda ba ya aikin komai amma yana da jirgin sama na kansa, ya mallaki gidaje a Dubai da Ingila saboda yana sayen dala a farashin kaza da kaza ya sayar". A cewarsa.
Ya faɗa cewa duk abun da aka yi a ƙasar nan shekaru takwas baya an yi su ne da kuɗin bashi. Inda ya ƙara da cewa babu wata ƙasa da za ta yi nasara a irin wannan tsarin tattalin arziƙi.
"Zan rarrashi al'umma ne su yi haƙuri su rungumi wannan matsi da ake ciki su yi rayuwarsu daidai matsayi da samunsu, kada mu yi rayuwar da ta fi ƙarfin samunmu a inda mutane ke neman abin da za su kai bakinsu. Waɗanda kuma za su iya taimakon masu ƙaramin ƙarfi su taimaka musu". Cewar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi.
0 Comments