Mun gode wa Allah raya mu da ya yi, da kuma lafiya da ya bamu, wannan yin Allah ne inji sheikh Zakzaky

Mun gode wa Allah raya mu da ya yi, da kuma lafiya da ya bamu, wannan yin Allah ne inji sheikh Zakzaky 

Sheikh Zakzaky yayinda yake gudanar da jawabi a wajen taron tarbarsa da ake gudanarwa Yanzu haka a Abuja

Yayin da yake jawabin godia ga Allah Daya basu lafiya kuma ya raya su shehun yace "Mun gode wa Allah raya mu da ya yi, da kuma lafiya da ya bamu, wannan yin Allah ne."

Sheikh din kuma ya bayar ga hakura ga mabiyan nashi akan dadewar da akai ana jiransu yace "Abin da Allah ya ƙaddara daidai ne ba mu so a ce an bar mutane sun jima suna jira ba, don haka muna neman afwar ƴan’uwa a kan hakan."

cikin jawabin Sheikh din yake cewa "Wani likita ma da ya gani Ihu ya yi ya ce: Ba yadda za a yi a ce wannan ya zama yana da rai, harsashi ƴan kuci-kuci har guda talatin da takwas (38) har da wasu a ƙwaƙwalwa, nake cewa Allah mai raya wa shi ne ya raya mu kawai."


Post a Comment

0 Comments