Nafi ƴan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa: Dangote

 Nafi ƴan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa: Dangote



Fitaccen attajiri kuma ɗan kasuwar Afrika Aliko Dangote yace ƴan Najeriya sun kafa masa ƙahon zuƙa suna son dole sai sun zuƙe masa jini, Ɗangote yace mafi yawan jama'a suna ganin tamkar yana da hannu a tsadar rayuwar da ake fama da ita a halin yanzu a ƙasar musamman tsadar kayan masarufi.

"Kai bari in gaya muku gaskiya wannan tsadar rayuwar daga Allah take shi kaɗai ne ke iya yaye mana ita amma akwai laifin gwamnatin tarayya, ni kaina nafi ƴan Najeriya shan wahalar wannan tsadar rayuwar saboda dukkan kayan da nake fitar wa tun daga Sugar, Fulawa, Siminti, Gishiri, Maggi, dukkansu da naira nake siyar wa da ƴan Najeriya su ni kuma da Dollar nake zuwa in shigo da kayan haɗinsu.

Dalar Amurkar nan kuma kowa ya san farashinta a halin yanzu ko mutum bai je makaranta ba ya san farashin dala a wannan lokaci, so ni kaina na rasa Market Control, idan na siyar wa dilolina kaya suka biyani da naira idan na canza ta zuwa dala sai inga nayi mummunar faɗuwa domin kuwa kuɗin basa isa ta in sake siyo kayan haɗin da nayi a baya balle ayi maganar riba.


Saboda haka don Allah kada kowa ya zargeni wannan matsalar duk gwamnatin tarayya ce ta haddasa ta, sakamakon janye hannunta daga bawa naira kariya, ta cire tallafin dala da kuma na man fetur duk a lokaci ɗaya, ina kira ga ƴan Najeriya tunda dai su suka fito suka zaɓi gwamnatin nan to su tabbatar tayi musu abinda suke so.

Koda ba'a mayar da tallafin mai ba to su roƙe ta data mayar da tallafin dala ina tabbatar musu ko shi kaɗai aka mayar duk farashin kayan nan zai rikito da kashi 60% cikin 100 da gaggawa idan kuma ba haka ba nan da zuwan watan biyar lokacin da gwamnatin nan zata cika shekara ɗaya da rantsarwa muna hasashen buhun Sugar a kamfani ma sai ya kai mana naira dubu 150" In ji shi kamar yadda ya bayyana a ɗazu

Muna roƙon Ubangiji Allah ya kawo mana sauƙin wannan lamari.


Hafsat Abdullahi   Muryar Labarai 

Post a Comment

0 Comments