Rarara Ya Nemi Alfarmar kotu Data dakatar da umarnin data bayar na Bayyanarsa a gaban kotu kamar yanda ta bada umarni a baya.

Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara Ya Nemi Alfarmar kotu Data dakatar da umarnin data bayar na Bayyanarsa a gaban kotu kamar yanda ta bada umarni a baya.



Mawaƙin Yace Mai Ƙararsa Kan Cin Zarafin Buhari Alhaji Sani Ahmad Yazubar masa da kima a idon Jama’ah saboda haka yana Roƙon babbar kotun data da dakatar da umarnin bayyanarsa a kotu kamar yanda karamar kotun ta bayar. 


Idan Baku Manta Ba A shekarar data gabata Ne Wani Masoyin Shugaban Ƙasa Buhari Mai Suna Sani Ahmad Ya Maka Mawaƙin Gaban Kotu kan Cin Mutuncin Tsohon shugaban ƙasar Inda Kotu ta aika masa da Sammaci Amman Mawaƙin Ya ɓuya Saidai aka Lika masa a Kofar Gidan sa daga bisa kuma Kotun ta bayar da Umarnin Ya bayyana Gabanta shi Saboda taka dokar ta.


A Yanzu Haka dai Mawaƙin Ya garzaya Babbar kotun Jahar Nasarawa dake Doma inda gabatar da Ƙorafinsa Yana buƙatar kotu ta Tsayar da Wannan Shari'a Har sai An canza Umarnin Bayyanar sa da Kotun ta bayar.

Post a Comment

0 Comments