Rashin Abba kyari a rundunar ƴansanda shine babban dalilin ta6ar6arewar tsaro a Najeriya inji wata Kungiyar malaman kirista.



 "Rashin DCP Abba Kyari A Rundunar Ƴansanda Shi Ne Babban Dalilan Taɓarɓarewar Tsaro A Najeriya", Cewar Ƙungiyar Malaman Addinin Kîriśta ta ƙasa.

Muryar Labarai  ta ruwaito cewa  mai magana da yawun ƙungiyar, Bishop Lawrence Ngene na bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Abuja.

Kamar yadda ya ce: "rashin babban jami'in ɗan'sanda Abba Ƙyari da tawagarsa a cikin rundunar ƴan'sanda ta ƙasa shi ne babban dalilin da ya haifar da taɓarɓarewar tsaron da ake gani yau a Najeriya". Cewar ƙungiyar.

Ƙungiyar ta manyan fada-fada da malaman addinin kirista ta ƙasa, "Nigerian Clerics Council Of Bishops and Imam" ta kuma ƙara da yin ƙira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ƴan majalissu da su yi ƙoƙarin mayar da DCP Abba Kyari da tawagarsa bakin aiki domin su cigaba da fatattakar ƴan ta'ádda.

Post a Comment

0 Comments