Rashin zaunawa Shari'ar ƴan uwa 60 a Abuja

Rashin zaunawa Shari'ar ƴan uwa 60 a Abuja.



Alkalin yayi zuciya saboda rashin halartar lauyan gwamnati inda ya ce bazai sake dawowa ba sai bayan sallah.

Tsawon lokaci alkalin dake shari'ar ƴan uwa 60 da ake tsare dasu Sama da shekara hudu a gidan yarin kuje har yau ankasa samun Zama domin yanke hukunci saboda zalunci.

Yau alƙali Sulaiman Belgore da Lauyan ƴan sanda DCP Simon lough sun haɗa baki don su cutar da ƴan uwan da ake tsare da su a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

An shirya cewa shari'ar yau za'a fara ta ne da misalin ƙarfe 12 na rana, alƙali Sulaiman Balgore ya zo kan lokaci, ya ɗauki dogon lokaci yana jira amma Lauyan Gwamnati bai zo ba, ana cikin haka ne alƙalin ya nuna ya yi zuciya yai tafiyar shi, ya ce kuma bazai sake dawowa ba sai bayan Sallah, wato dai nan da wasu watanni masu zuwa, alƙali na juyawa da motarsa zai tafi sai ga Lauyan ƴan sandan shi ma yana shigowa, amma a haka alƙalin ya ƙi yarda ya tsaya, wadda hakan ya nuna dama sun tsara su yi zaluncinsu ne da suka saba ta wannan sigar. In ba haka ba sau nawa alƙalin yana zuwa ya yi jira na sama da awa ɗaya kafin zuwan Lauyan ƴan sandan? Ko a zaman karshe da kotun ta yi sai da alƙalin ya yi jiran sama da awa ɗaya kafin zuwan Lauyan ƴan sandan.

 A daidai wannan lokaci da ake ganin wannan Shari'a tana gab da ƙarewa su kuma azzalumai sun fito da wani sabon salon zalunci, don haka akwai bukatar ƴan uwa su canja nasu salon su ma na taimakon waɗannan raunanan bayi da ake tsare da su bisa zalunci da sunan Shari'a. 

 Ƴan uwa su nunka addu'oinsu na neman mafita ga mazlumai, da kuma tsinuwa da neman taɓewar Azzalumai, sannan kuma mu yi duk abinda za mu iya yi wajen bayyana ma duniya kalar muguntar da ake ma ƴan uwan mu.

 Ya Allah ka gaggauta kawo ma bayinka mafita, ka yanke duk wani jin ɗaɗi na azzalumai.

Post a Comment

0 Comments