Sheikh Zakzaky ya halarci taron Nisfu Sha'aban a Abuja.
Daga Mahadi Umar kaita
Jagoran Harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibraheem Zakzaky ya samu halartar kwatanccen taron da mabiya mazhabar ja'afariyya suka Saba shiryawa a duk ranar 15 ga watan Sha'aban Wanda akema ranar lakabi da bikin nusfu Sha'aban.
Taron Wanda Yan gwagwarmayar tabbatar da Addini a karkashin jagoranchin sheikh Zakzaky suka Saba shiryawa a Zaria kafin afkuwar kisan kiyashin na Zaria Wanda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta jagoranta.
Taron na Bana yazo da wasu sauye sauye domin ba'ayi tsammanin sheikh din zai samu halartar taron ba Amman cikin iKon Allah sai gashi ya halarta dukda bai Jima da dawowa daga jinya ba Amman a haka ya daure ya halarta domin faranta ran mabiyan nashi.
Saidai ta wata fuskar halartar Sheikh din ba abun mamaki bane duba da yacce yake matukar kaunar mabiyan nashi domin har kasar Iran saida ta bukaci ya tsaya ayi taron bikin ya kasance a matsayin babban Bako Amman sheikh din yace Shima wannan Rana tanada Matukar anfani a gareshi Hakan yasa ya dawo kasar domin ayi bikin dashi cikin Almajiransa.
Photo credit/ yantandu photography
Nusfu Sha'aban
Ranar 15 ga watan Sha'aban Rana ce wacce aka haifi Muhammad Mahdi bin Hassan Al askari, kamar dai yacce aka sani Yan Shi'a sukan raya dukkanin al'amurran iyalan gidan Manzon Rahma to haka ma 15 ga watan Sha'aban ya kasance ranar da aka haifi Muhammad Mahdi Wanda jika ne wajen manzon Allah (SAW) Kuma shine limamin wannan zamanin da muke ciki.
Haka zalika a wajen Yan Shi'a Yan gwagwarmaya a Najeriya yau takasance Rana mai mahinmanchi a garesu domin kuwa a daidai irin wannan ranar aka haifi Sheikh Zakzaky jagorar harkar wannan dalilin yasa akan hada bukuwan biyu a lokaci Daya.
0 Comments