Sheikh Zakzaky ya mayar da martani Akan masu mashi izgili akan Maganar da yayi ta buraguzan Harsashin dake cikin kanshi

 Sheikh Zakzaky ya mayar da martani Akan masu mashi izgili akan Maganar da yayi ta buraguzan Harsashin dake cikin kanshi

Sheikh Ibraheem Zakzaky a ranar da ya dawo gida bayan tafiyar jinya ta tsawon wata hudu da yayi. Photo credit: cibiyar wallafa

Daga Mahadi Umar kaita

Sheikh yayi maganar ne a ranar bikin Nusfu Sha'aban a gidansa dake Abuja yayin ganawarshi da wasu almajiransa a nasa jawabin Sheikh din yake cewa wannan yin Allah ne Kuma babu abunda ya gagari Allah, Kuma wannan ya faru tun daga mutanen farko idan sukaga ayar Allah sai su koma suna izgili maimakon suyi imani don haka wannan ba bakon abu bane ba ga Wanda ya rike gaskiya. Saboda izgili suna cewa harsashi 38 bayan sunsan ba harsashi nace ba baraguzai nace Yan kuci-kuci guda 38, nasan babu yacce za'ai harsashi 38 ya zauna a kai domin nasan kasan ni ba mahaukaci bane ba Na fi ka Ilimin Addini, Bokon ma na fi ka kuma na girme ka bazanyi magana marar Ma'ana ba, na lura mutanen nan suna Jin haushin Allah ya barni da raina. Inji sheikh din a jawabin nasa na ranar lahadi 27 ga watan February.

Wannan dai bashine karo na farko da al'umman arewacin kasar suke mashi izgili ba Akan wasu ayoyi da Allah ya nuna Akan shehun malamin a lokacin da gwamnatin Najeriya karkashin mulkin Muhammadu Buhari ta afka masu a December din 2015 a gidansa dake Gyallesu Zaria.

Video: yacce sheikh Zakzaky ya mayarda martani cikin hikima da balagar zance


Akwai abubuwan ban al'ajabi da suka faru da sheikh din a lokacin cikin hikimar Allah.

Bayan da sojojin Najeriya sukayi ruwan wuta a jikin sheikh din sun dauki gawarshi a matsayin matacce Wanda Allah cikin ludufinsa ya farfado dashi Wanda hakan ya tsoratar da sojojin da suke a wajen.

Hadda idonshi guda daya Saida ya tsiyaye saboda harsashin da aka harba mashi a cikin idon Wanda a lokachin kwayar idon sheikh din Saida ta zube baki daya amman cikin iKon Allah yanzu haka sheikh din idon Nashi ya dawo kamar wanda hakan bai faru dashi ba.

Sheikh Zakzaky lokacin da suka fita jinya kasar India a Shekar 2018

Akwai abubuwan al'ajabi masu yawan gaske Wanda suka faru da Sheikh din Wanda babu wanda zai iya yinsu saidai Allah.


Post a Comment

0 Comments