Shekaru uku da rasuwar Farfesa Dahiru Yahaya
Muna addu'ar Allah ya jikansa da Rahama.
Fafesa Dahiru Yahaya Malamin Jami'a ne kuma masanin tarihi. Kuma Malamin Malamai ne da ya kware a fanninsa. Kafin rasuwarsa ya kasance Fafesa ne a sashen nazarin tarihi a jami'oin Bayero dake Kano da Ahmadu Bello dake Zariya.
Bayanai sun nuna cewa an haife shi ne a garin Kano a ranar 30 ga wata Yunin 1947. Ya yi karatun digirinsa na farko a bangaren nazarin tarihi a Kwalejin Bayero (Jami'ar Ahmadu Bello a yau) a shekarar 1970. Ya kammala digirin digirgir dinsa ne a bangaren diflomasiyyar tarihi a Jami'ar Birmingham dake Birtaniya a 1975.
Ya yi aiki a matsayin mataimaki na jin dadi da walwalar jama’a a karkashin gwamnatin yankin Arewa da ke Kaduna. Sannan ya yi aiki a matsayin jami’in gudanarwa a karkashin gwamnatin jihar Kano.
Dahiru Yahaya ya soma karantawa ne a sashen nazarin tarihi dake Tsangyar Fasaha da nazarin addinin Musulunci na Jami’ar Bayero ta Kano a shekarar 1970 inda ya yi aiki na tsawon rayuwarsa.
Ya rasu ne a ranar Laraba 3 ga watan Fabarairun 2021 bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a jihar Kanon Nijeriya.
Ya rasu yana da mata 3 da 'ya'ya 24.
0 Comments