Shin Miya jago aka cima young sheikh mutuminci a yayinda yazo yin magana a bainar jama'a ?

Shin Miya jago aka cima young sheikh mutuminci a yayinda yazo yin magana a bainar jama'a ?👇



A taron an gayyace shi ne dan yai magana, matsayin sa na É—an Darika, kuma  taron na  Darika ne kamar yacce aka shaidawa wakilinmu

Bayan young sheikh ya amshi abun magana a cikin maganar tasa Young Shiekh yake cewa a "lokacin Sheikh Ibrahim Inyass yana kaiwa kafirai ziyara kuma yana zaman lafiya dasu."

Sai yake cewa dan haka ba daidai bane abinda ke faruwa tsakanin Æ´an DARIKA da yan IZALA.

Yace tunda har maulan mu Ibrahim Inyass zai zaman lafiya da kafiri ma, me yasa zamu rinƙa gaba da yan uwan mu da suke fadar kalmar La'ilaha ILLaLLAHU?

Nan take wani tsoho ya karɓi abin magana yace: Ba Young Shiekh ba ko Old Sheikh ne, munji abinda ka fada, dan haka bazai yiwu kazo ka tara dattijan mu kana fada musu magana ba.

Taya zakace da yan izala damu daya ne, kana nufin ba akan dai dai muke ba? To daga yau ba zamu kara bari kai mana wannan abin ba.

Yace Young mun gode Allah yasa nan gaba ka dawo namu.

Abin Haushin shine yadda suka juyar da gaskiya zuwa karya, shi isa bana bari aƙidar Addini ta rufen ido shi isa ma Ni har yanzu Ban tantance dan wanne kungiyar addini bane domin hakan yana sa munafurci da ƙin gaskiya wallahi.

Duk mutumin kuwa da yace lallai sai kungiya kaza to wataran zai ga gaskiya a waccan kungiyar yace karya ce wanda hakan kuma saɓawa uban giji ne.

Kawai ka tsaya matsayin ka na musulmi duk inda kaji gaskiya daga bakin Allah da Manzon sa ka É—auka, karka duba wa ya faÉ—a.

Allah yasa mu dace

Daga: Salisu Magaji Fandalla'fih

Post a Comment

0 Comments