Shugaban Hisba A Jahar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ya Yi Murabus daga mukaminsa

Shugaban Hisba A Jahar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Ya Yi Murabus daga mukaminsa

Daga Mohammad A. Isa

Rahotannin daga Jihar Kano na tabbatarwa Zamani Media cewar, Shahararren Malamin Addinin Islama mai jan ragamar Rundunar Hizba a matsayin Kwamandanta a jihar Kano, Shaikh Aminu Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hukumar.

Kamar yadda wasu bayanai suka bayyanar, murabus din na zuwa ne sakamakon sakin da aka yi wa yarinyar nan wadda ta yi kaurin suna a shafukan sada zumunta wajen sheke aya, Murja Kunya daga gidan Kaso bayan da aka aka garkame ta, lamarin da ake zargin wasu wadanda suka daure mata gindi daga manya ne suka yi ruwa suka yi tsaki a cikin sakin, wanda hakan ya sa6a wa Ka'ida da Doka.

Ya zuwa yanzu dai, Shaikh Daurawa bai yi cikakken bayani kan dalilin murabus din nasa ba tukunna.

Post a Comment

0 Comments