Shugabar Ƙasar Hungary Tayi Murabus Saboda Zargin Yiwa Wani Mai Fyaɗé Afuwa



Shugaba Katalin Novak ta ƙasar Hungary ta sanar da yin murabus a jiya Asabar, bayan da ta fuskanci matsin lamba kan yin afuwa ga wani mutum da aka samu da laifin taimakawa wajen boye wata shari'ar cin zarafin mata a gidan yara.

Mahanga ta ruwaito shugabar na cewa "Na yi kuskure... amma kuyi mani afuwa kuma yau ce rana ta ƙarshe da zan yi maku jawabi a matsayin shugabar ƙasa," in ji Novak a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar.

Shin kuna ganin cewa irin hakan zai iya faruwa a Najeriya?


Post a Comment

0 Comments