Sojojin ruwan Yaman sun lalata wani jirgin ruwa na Burtaniya a mashigin tekun Aden.

 Sojojin ruwan Yaman sun lalata wani jirgin ruwa na Burtaniya a mashigin tekun Aden

 Wannan dai shi ne jirgin ruwa na Birtaniya na uku da Yemen ta kai wa hari a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

Daga Mahadi Umar kaita

 A ranar 19 ga watan Fabrairu ne dakarun kasar Yemen suka sanar da kai wani sabon hari kan wani jirgin ruwan kasuwanci na kasar Burtaniya a mashigin tekun Aden.

  Kakakin rundunar Yahya Saree a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce "Dakarun sojin ruwa na Dakarun Yaman... sun kai wani gagarumin farmakin soji, inda suka auka wa wani jirgin ruwan Burtaniya a mashigin tekun Aden RUBYMAR da makamai masu linzami na ruwa."

  "Jirgin ya samu mummunar ɓarna wanda ya sa ya tsaya gaba ɗaya.Sakamakon ɓarnar da jirgin ya samu, yanzu yana cikin haɗarin nutsewa a mashigin tekun Aden. Mun tabbatar da cewa ma'aikatan jirgin sun fita lafiya a lokacin da ake gudanar da aikin," in ji Saree.

 Hukumomin ruwa na Birtaniya sun ce an fara gudanar da bincike bayan rahotannin fashewar wani abu kusa da wani jirgin ruwa na Biritaniya a ranar Lahadi.


Post a Comment

0 Comments