Taƙaitaccen tarihin Imamu Musa Alkazim Imami na bakwai daga cikin limamai Sha biyu da mabiya marhabar ja'afariyya ke bi.

Tunawa da Shahadar  Imam Musa Alkazim (A.S)



Imam Musa al-Kazim (wanda aka fi sani da Abul Hasan).

Shine Imami na bakwai daga cikin limamai Sha biyu da mabiya marhabar ja'afariyya ke bi.

An haife shi 6/November/744 a birnin Madina na ƙasar Saudiyya.Ya rasu a ranar 25 ga watan Rajab shekara ta 799 miladiyya a birnin Bagadaza na kasar Iraqi.

Imam Kazim shine ɗan Imami na shida Imam Jafar Sadik, kuma jikan Imami na biyar Imam Muhammad al-Baqir.

Yana daga cikin zuriyar Annabi Muhammad ta wajen ƴar sa Fatima da kawunsa kuma surukinsa Ali ibn Abi Talib.

Imam Musa al-Kazim ya shahara da dimbin ilimi da hikima, kuma ana masa kallon daya daga cikin manyan limaman Ahlulbaiti (iyalan Annabi Muhammad).

Sannan kuma ya shahara da taƙawa da hakuri da kyautatawa, kuma ana tunawa da shi a kan muhimmancin ilimi A lokacin rayuwarsa Imam Musa al-Kazim ya fuskanci ƙalubale da wahalhalu da dama.

Halifofin Abbasiyawa ne suka sanya masa ido, suna ganinsa a matsayin barazana ga mulkinsu sun ɗaure shi na tsawon lokaci a gidan yari ana azabtar da shi, duk da haka ya tsaya tsayin daka a kan imaninsa ya ci gaba da koyarwa da yaɗa saƙon Musulunci.

Daya daga cikin shahararrun tarihin Imam Kazim shi ne na haduwar sa da Harunar Rashid, halifan Abbasiyawa. Harun al-Rashid ya zargi Imam Kazim da shirya masa maƙarƙashiya tare da sanya shi kurkuku a wani gidan kurkuku a Bagadaza.

A lokacin da yake tsare Imam Kazim ya samu ziyarta ɗaya daga cikin sahabban Haruna Rashid, wanda ya shaida hakurin Imam da takawa da karantarwar sa.

Daga karshe dai wannan sahabin ya zama mabiyin Imam Kazim, daga baya kuma ya shaida cewa ba shi da laifi.

Imam Kazim ya rasu a gidan yari a ranar 25 ga watan Rajab shekara ta 799 miladiyya, Mutuwarsa ta kasance sakamakon gubar da aka bashi, wanda kusan halifofin Abbasiyawa ne suka bashi.

An bizne shi a Masallacin Yassin dake Baghdad ƙasar Iraqi.



Post a Comment

0 Comments