Tarihi: Tunawa da Shahadar imam musal khazim (AS)

Imam khazim yasha wahala sosai a hannun azzaluman da suka daureshi.

Tarihi: Tunawa da Shahadar imam musal khazim (AS)

“Na farko an kaima kalifan wannan lokacin Haruna wanda wasu mutane suke ce dashi wai Rashid. An kai masa tsegumin cewa ai shi Imam khazim mutane suna zuwa gareshi shine jagoran su, shine kalifan su, kuma har yana ƙarɓan mubaya’ar su. Don haka shi Haruna ya tashi daga Bagadad ya tafi birnin Madina‚ lokacin da suka je se su rankaya da shi Imam khazim zuwa ƙabarin Manzon Allah (S.a.w.w) don ziyara. To‚ se shi Harunan ya gabata yace ma Manzon Allah “Assalamu Alaika Yabni Ammi Ya Rasulullah” Haruna bayan ya gama Imam khazim ya gabata yace “Assalamu Alaika Abbati Ya Rasulullah” sai ya dube shi yace a‚a‘ ya zakace baban ka ne? Ai ɗan ammin kane saboda da duk cikan mu mu ai ’ya’yan Abdul mu ɗallib ne, mu ’ya’yan Abbas ku kuma ’ya’yan Abu talib saboda haka kaga duk cikan mu shi manzon Allah ɗin nan ɗan ammim mune.”

“Se yace in abin Manzon Allah ya dawo duniyan nan ne in ya biɗi auren ɗiyarka zaka bashi? Sai yace kwarai kuwa. Se yace kana ganin ze iya yuwuwa ya biɗi auren ɗiyata? To‚ anan se Haruna yayi shiru yaji haushi don yasan cewa shi Imam khazim jikan fatimatuz Zahara (S.a) ne, kuma ainihin ɗa na tsatso ta hanyar 'Ya mace ko ta hanyar Ɗa namiji haramun ne ga mutum kamar yadda ’Ya ta haramta haka ’yar ko jikanyar ’Ya har ya zuwa tashin ƙiyama, mai makon shi Haruna ya fahimci gaskiya ne shi ya faɗa daya ce “Assalamu Alaika Ya Abbati Ya Rasulullah” yasan cewa Manzon Allah uba yake ga Imam khazim amma ba uban Harun bane, yaji haushi ya shirya cewa a fita dashi mutane sun sanya ido ina za'a tafi dashi? A sanya ƙafila ta hanyar Bagadad da tayi nisa sai ta juya hanyar Basara, saboda haka mutane suna da yaƙinin an kaishi Bagadad ne, nan ko ya aika dashi Basara ne.”

Zamu ci gaba da tsakurowa Insha Allah....



Post a Comment

0 Comments