Wata kungiya a Kano ta bukaci a rusa masarautu, a mayar da Khalifa Sanusi
Wata kungiya a jihar Kano ta yi kira da a rusa masarautun jihar Kano guda hudu sannan a mayar da tsohon sarki Muhammadu Sanusi na II a matsayin sabon sarkin Kano.
A wata sanarwa, kungiyar mai suna 'Yan Dangwalen Kano ta bukaci gwamnan Kano da majalisar dokokin jihar su duba sashen dokar da ya tsaga masarautar Kano zuwa masarutu guda biyar.
Kungiyar ta ce masarauta guda daya kamar yadda take a baya zai taimaka wajen tafiyar da harkar sarauta ba tare da rarrabuwar kai ba. Sannan hakan zai samar da zaman lafiya mai dorewa.
Dangane da tsohon sarki, Muhamamdu Sanusi II, sanarwar ta ce "bisa girmamawa muna kira ga majalisar dokoki ta jihar Kano da ta yi waiwaye dangane da sashen dokar da ya kwabe Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki. Mun yi amannar cewar tunbuke Sanusi Lamido Sanusi ya haifar da rashin zaman lafiya a jihar".
Daga karshe kungiyar ta bukaci majalisar dokokin da ta yi duba kan bukatunta domin ci gaba da karuwar arzikin al'ummar Kano.
0 Comments