Yacce Wani yaro Dan baiwa ya Kirkiri Motar Kwali Dake Tafiya Gaba Da Baya Batare Da Amfani Da Wata Na'urar Batureba
Wani Dan Makarantar Firamare Ya Kirkiri Motar Kwali Dake Tafiya Gaba Da Baya Batare Da Amfani Da Wata Na'urar Batureba A Garin Kankara
Dalibin Mai Suna Hamza Ahmed Mai kimanin shekaru 12 da haihuwa dan aji biyar a Makarantar Uncle D Memeorial International Primary School Kankara, ya kirki wata motar kwali datake tafiya batare da sakamata Wani abu daya shafi na'urar batureba.
Ayayin zantawar wakilin mu da wannan yaron ya bayyana cewa ya fara tunanin ya kirkirar wannan mota awani lokaci daya taba ganin wani yayi makammanciyar irin wannan motar ne.
Dalibi Hamza Ahmed ya cigaba da cewa yayanayin amfani da kwali amatsayin gangar motar da murafan lemun roba Amatsayin tayoyin sai kuma tsintsiyar kwakwa amatsayin Sandar tuki wato steering kamar yadda kuke Ani ahotunan da muka dora maku.
Abin mamaki motar duk da Bata amfani da wata na'urar batureba amma takan juya dama zuwa dama ta hanyar juya abinda ke hannun direba tamkar motar gaske.
Allah ya kara basira da Kuma fatan Gwamnati zata ringa taimakawa irin masu basira
0 Comments