Yadda jami'an ma’aikatan lafiya ke aiki cikin hatsari a jihar Adamawa

Yadda jam'ian ma’aikatan lafiya ke aiki cikin hatsari a jihar Adamawa



Ma’aikaciyar rigakafi, Dorothy Ezikiel, ta ce ‘’nakan tafi Mayo da Gombi, wadanda suke kimanin sa’a biyu daga wurin da nake zaune. Kafin na tafi, nakan yi addu’ar Allah Ya kare ni.’’

Suna aiki a wani asibitin al’umma a wani wuri da bai da nisa daga tsakiyar birnin Yola na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya.


Damuwar da suke da ita kan tsawon lokaci da suke kwashewa a kan hanya ba ta kai irin damuwar da suke da ita game da hatsarin da za su iya shiga a hanyar ba.


A zantawa da TRT Afrika, ma’aikaciyar rigakafi, Dorothy Ezikiel, ta ce ‘’nakan tafi Mayo da Gombi, wadanda suke kimanin sa’a biyu daga wurin da nake zaune. Kafin na tafi, nakan yi addu’ar Allah Ya kare ni.’’


A cewar Dorothy mai shekaru 26, ‘’na san ina yin babbar kasada, domin za ka iya shiga hannun masu garkuwa da mutane ko ma ‘yan ta’adda idan kana tafiya a hanyar mota zuwa yankunan karkara.’’


A shekarun baya-bayan nan matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa ta karu musamman a arewacin kasar.


Alkaluma daga cibiyar kwararru kan hulda da kasashen waje da ake kira Council on Foreign Relations wadda ke da mazauni a Amurka, na nuna cewa an yi garkuwa da mutum fiye da 4,000 a Nijeriya a 2022 yayin da aka kashe sama da 4,500.


A 2018, Boko Haram ta yi garkuwa da ma’aikatan agaji mata su uku a jihar Borno mai makwabtaka da Adamawa.


A watan Yunin 2022, babban jami’in ayyukan jin kan bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya a Nijeriya ya shaida wa kafofin labarai na cikin gida cewa yawan kai hare-hare a kan ma’aikatan agaji, musamman a jihar Adamawa da yankuna masu makwabtaka da ita a arewa maso gabashin kasar, na kawar da hankali daga ayyukan agaji.


Duk da hatsari ga rayuwarsu, ma’aikatan lafiya a wadannan yankuna na ci gaba da taimaka wa jama’a, suna shiga lunguna, wasunsu masu wuyan zuwa, domin ayyukan rigakafi da ake matukar bukata da kuma rarraba magunguna.


Lokaci mai ban tsoro


John Manabeta, Daraktan Zattaswa na wata kungiyar fafutikar kare hakkin mata, yana mamakin irin karfin hali da ma’aikatan lafiya ke ayyukan duk da hatsarin da suke fuskanta.


‘’Su kadai suke zuwa wadannan kauyukan. Ba su tafiya da rakiyar jami’an tsaro … babu komai. Sukan dai yi fatan komawa gida lafiya’’ a cewarsa.


Shiga yankuna masu hatsari ba shi ne kadai ke damun ma’aikatan lafiya ba. Suna kuma fuskantar kalubale daga masu adawa da rigakafi a arewacin Nijeriya, wadanda a wasu lokutan kan nuna tirjiya har ta hanyar tashin hankali ga ma’aikatan lafiyar.

Post a Comment

0 Comments