Yan Bindiga Sun Kai Hari Sun Kashe Dan Sanda A Zamfara

 Yan Bindiga Sun Kai  Hari Sun Kashe Dan Sanda A Zamfara



Daga Abbakar Aleeyu Anache 

Rahotanni daga jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa yan Bindiga sun kai hari shingen binciken yan sanda dake kauyen Tazame inda suka harbe dan sanda daya har lahira tare da raunata wasu.

Shingen na da nisan kilomita daya zuwa garin Kwatarkwashi, wanda ke kusa da Gusau, babban birnin jihar.

Majiyoyi da dama sun shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sama da 40, tare da bude wa shingen wuta da misalin karfe 4 na safiyar ranar Lahadi.

Majiyar ta ce maharan sun kuma banka wa shingen wuta tare da kone komai kafin daga bisani suka tsere zuwa daji.

Mun yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, domin jin ta bakinsa, ya ci tura, domin bai amsa kiran da aka masa ba.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa da ke ci gaba da fuskantar kazaman hare-haren ta’addancin ’yan bindiga.

Post a Comment

0 Comments